'Yan tawaye 4 aka kashe a wani rikici da suka fafata da jami'an tsaro a yankin Jammu Kashmir na Indiya.
Jami'an 'yan sandan Jammu-Kashmir sun ce bayan jami'an soji ne suka kai farmaki a yankin Pinjora da ke Shopian bayan bayanan sirri da suka samu.
Sanarwar ta ce a yayin farmakan mayakan kungiyar 'yan tawaye ta Hizbul Mujahidun sun yi arangama da jami'an tsaro inda aka kashe 4 daga cikinsu.
An bayyana jikkata wasu jami'an tsaro 3.
A cikin awanni 24 da suka gabata an samu arangama sau 2 tsakanin jami'an tsaro da 'yan tawaye a yankin Jammu Kashmir.