'Yan sanda 3 sun rasa rayukansu sakamakon skamakon harin bam da aka kai da wata mota a gundumar Shahweli Kot da ke jihar Kandahar din Afganistan.
Kakakin Fadar Gwamnan Kandahar Bahir Ahmadi ya shaida cewar maharin ya nufi cibiyar 'yan sandan gundumar Shahweli Kot.
Bayanan farko da aka samu sun bayyana mutuwar mutane 3, kuma babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
Ahmadi ya kara da cewar saboda karar fashewar bama-baman da ke cikin motar, gine-ginen da ke yankin sai da suka motsa inda wasun su suka samu matsala.