An kashe 'yan tawayen Taliban 31 sakamakon wani farmaki da aka kai musu a arewacin Afganistan.
Sanarwar da Runduna ta 209 ta fitar ta ce, jami'an tsaron Afganistan sun kaiwa 'yan tawayen farmaki a gundumar Belh da ke garin Mezarissharif.
A farmakin an kashe 'yan tawayen Taliban 31, an kuma kwace garin Belh daga hannun 'yan ta'addar.
Sanarwar ta kara da cewa, an kuma nesanta 'yan tawayen daga garin Mezarissharif.