Rundunar sojin Yaman ta sanar da kashe 'yan tawayen Houthi 6 da suka hada da jagororinsu a wata arangama da suka yi a lardin Hudeyde.
Dakarun Amalika na Rundunar Sojin Yaman sun sanar da hana 'yan tawayen Houthi shiga yankin Tahite na Hudeyde wanda ya janyo barkewar arangama.
An bayyana kashe mayakan Houthi 6 da suka hada da wasu jagororinsu inda aka jikkata wasun su da dama.
Bangaren Houthi bai ce komai ba game da batun.