Rundunar Sojin Yaman ta bayyana cewar sun kashe 'yan tawayen Houthi 5 a wata arangama da suka yi a garin Hudeyde.
Sanarwar da aka fitar daga ofishin yada labarai na mayakan Amalika da ke da alaka da Rundunar Sojin ta Yaman ta ce an kashe 'yan tawayen Houthi 5 sakamakon arangamar da ta afku a lokacin da suka yi kokarin shiga yankunan da ke hannun sojin gwamnati a gundumar Tuhaita ta lardin Hudeyde.
Sanarwar ba ta bayyana ko an kashe wani jami'in tsaron gwamnati ba.