Dakarun sojin Turkiyya sun kai farmakai ta sama tare da kashe 'yan ta'addar a ware na PKK 4 a arewacin Iraki.
Sanarwar da aka fitar daga shafin sada zumunta na yanar gizo na Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta ce "Sakamakon farmakanmu da muke ci gaba da kaddamarwa, an kai farmaki ta sama tare da kashe 'yan ta'addar a ware na PKK 4 a yankin Zap na arewacin Iraki. Za a ci gaba da kai farmakan har sai na ga bayan 'yan ta'addar."
Turkiyya na yaki da 'yan ta'addar a ware na PKK a ciki da wajenta.