An kashe wasu 'yan ta'addar a ware na PKK 4 a lokacin da suka yi yunkurin kai hari a yankin Farmakan Tsaron Firat dake arewacin Siriya.
Ma'aikatar Tsaron Kasa ta Turkiyya ta ce,
"An gano 'yan ta'addar PKK/YPG 4 na shirin kai hari a yankin Farmakan Tsaron Firat dake arewacin Siriya, kuma jaruman dakarunmu sun kassara su. Za a ci gaba da kai farmakai a yankin har sai an tabbatar da samar da zaman lafiya."