An kashe 'yan ta'addan da Iran ke goyawa baya 27 a Siriya

An sanar da cewa wasu jiragen yaki da ba'a san ko nasu wanene ba sun kai hari akan sansanonin 'yan ta'addan da Iran ke goyabaya a gabashin Deyrizor dake kasar Siriya.

An bayyana cewa 'yan ta'adda 27 aka kashe a yankin dai dake hannun gwamnatin Bashar Asad.

Kamar yadda wasu kafafe suka sanar wani sojan kare juyin juhanin Iran wanda kuma kwamanda ne a garin Albukemal ya mutu.

Kawo yanzu dai ba'a gano wadanda suka kai harin ba.

 


News Source:   ()