'Yan sanda 7 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a gundumar Almar da ke jihar Faryab din Afganistan.
Kakakin helkwatar 'yan sandan Faryab Abdul Karim Yurish ya shaida cewa, wani bam da aka ajje a gefen hanya a tsakiyar Almar ne ya fashe a lokacin da motar 'yan sanda ke wucewa.
Yurish ya ce, 'yan sanda 7 sun mutu sakamakon lamarin.
Babu wanda ya dauk alhakin kai harin.