'Yan sanda 3 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kaiwa shingen binciken ababan hawansu a jihar Gazne da ke Afganistan.
Wasu mutane da ba a san ko su waye ba ne suka kai harin kan cibiyar 'yan sanda da ke yanki na 4 na Gazne.
Kakakin Helkwatar 'Yan sandan Gazne Ahmad Han Siret ya shaida cewa, 'yan sanda 3 sun mutu sakamakon harin, kuma maharan sun ranta a na kare.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.