An kashe ƴan rajin ƙare muhalli sama da dubu 2

An kashe ƴan rajin ƙare muhalli sama da dubu 2

Rahoton ƙungiyar ta Global Witness da aka wallafa a jiya Talata, ya ce cikin shekarar bara ta 2023 kaɗai, masu fafutukar kare muhallin 196 aka kashe a sassan duniya.

Colombia ce dai ke zaman ƙasa mafi hatsari ga masu rajin na kare muhalli, inda a jimilce aka kashe 79 daga cikinsu a bara.

Sauran kasashen da aka samu salwantar rayukan masu ƙoƙarin bai wa muhalli kariya sun haɗa da Brazil, inda aka kashe masu fafutukar 25, sai Mexico da Honduras da a cikin kowannensu aka aka kashe ‘yan fafutukar sha takwas.

A matakin nahiya ko yanki kuwa, Kudancin Amurka ko Latin ke kan gaba wajen zama mafi hatsari, ko kuma lahira kusa ga masu fafutukar kare muhalli a duniya, inda a shekarar bara kaɗai aka kashe jimillar jami’ai 166, 54 a Mexico da Amurka ta Tsakiya, sai kuma 112 a Kudancin Amurka.

Ƙungiyar Global Witness ta bukaci gwamnatoci da su dauki ƙwararan matakai don bai wa masu kare muhalli tsaro tare da magance matsalolin da ke haifar da tashe-tashen hankula masu nasaba da sauyin yanayi da muhalli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)