Rahotan RSF na shekara-shekara ɗa aka wallafa a wannan Alhamis 12 ga watan Disamba, Sojojin Isra'ila ne ke da alhakin mutuwar ƴan jarida goma sha takwas a wannan shekara, inda suka kashe 16 a Gaza da 2 kuma a ƙasar Lebanon.
Rahotona ya ce, yankin Falasdinu shine mafi hatsari ga aikin ƴan jarida, inda aka samu adaɗi mafi yawa da manema labarai da suka mutu fiye da kowace ƙasa cikin shekaru biyar.
RSF ta ce fiye da ƴan jarida 145 sojojin Isra'ila suka kashe jummala tun daga watan Oktoba 2023 a Gaza, amma 35 ne suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.
Ƙungiyar IFJ
A na ta alƙaluma ƙungiyar jaridu ta International Federation for Journalist da ta wallafa nata rahotan a ranar 10 ga watan Disamba, ta ce ƴan jarida 104 aka kashe a sassan duniya cikin shekarar 2024, fiye da rabinsu a kuwa an kashe su ne a yankun Gaza.
Alƙaluman sun bambanta tsakanin IFJ da RSF saboda rashin jituwa kan hanyar tattara bayanan. RSF ta lissafa ƴan jarida ne kawai da ta tabbatar da cewa an kashe su a bakin aikinsu.
Tuni ƙungiyar RSF ta shigar da korafe-korafe guda hudu ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC kan laifun yaƙi da sojojin Isra'ila suka aikata masamman kan ƴan jarida.
Bayaga mutuwar ƴan jaridu 16 a Gaza, ƙungiyar ta ce wuraren da aka fi kashe ƴan jarida a shekarar 2024 sun hada da Pakistan da aka kashe 7 da Bangladesh da Mexico da aka kashe ƴan jaridu biyar-biyar kowannensu.
A cikin shekaru 25, an kashe ma’aikatan yada labarai 160 a Mexico bisa ga kididdigar da Frédéric Saliba, tsohon wakilin jaridar Le Monde, sai dai sabon shugaban ƙasar ya yi alkawarin sa ido kan tsarin shari’a don tabbatar da gudanar da bincike na hakika kan laifukan da suka shafi cin zarafin ƴan jarida musamman a matakin ƙananan hukumomi tare da masu gabatar da ƙara.
A shekarar 2023, adaɗin ƴan jaridan da aka kashe a duniya ya kai 55.
'Yan jarida 550 na tsare a gidan yari
Baya ga ƴan jaridar da aka kashe, RSF ta kuma fitar da alƙaluman wadanda aka daure a gidan yari, wanda ta ce ya kai 550 a duniya daga ranar ɗaya ga watan Disambar 2024, tsaɓanin 513 da ake tsare da su a bara.
Manyan ƙasashe uku da suka fi ɗaure ƴan jarida su ne China da 124, Hong Kong na da 11, akwai 61 a Myanmar sai 14 a gidajen yarin Isra’ila.
Bugu da kari, a halin yanzu an yi garkuwa da ƴan jarida 55, biyu daga cikinsu an yi garkuwa da su a shekarar 2024. Kusan rabinsu na hannun ƙungiyar IS.
A kwai ƴan jarida 95 da suka bace a sassan duniya, ciki har wasu hudu a wannan shekarar ta 2024.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI