An kashe akalla mutane 5 a harin bam a Resulayn

An kashe akalla mutane 5 a harin bam a Resulayn

Akalla mutane 5 ne sukıa rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai da wata mota a shingen binciken ababan hawa a yankin Resulayn da ke hannun 'yan adawar Siriya.

Rahotanni sun ce wasu fararen hula 12 sun samu raunuka.

Bam din ya fashe a kauyen Tel halaf na gundumar Resulayn da Dakarun Sojin Turkiyya da Mayakan Kasa na Siriya suka raba da 'yan ta'adda a karkashin Farmakan Taflkin Zaman Lafiya.

Sakamakon tashin bam din da ke cikin motar akori-kura da aka ajje a kusa da wani shingen binciken ababan hawa, mutane 5 sun mutu inda fararen hula 12 suka jikkata wadanda 3 daga ciki suke cikin halin rai mutu kwakwai.

Ana fargabar yiwuwar karuwar adadin wadanda za su mutu da jikkata sakamakon harin.

Jami'an tsaron yankin da suka fara gudanar da bincike sun bayyana cewar ana kyautata zaton 'yan ta'addar a ware na YPG/PKK ne suka kai harin.

A karo na karshe a ranar 26 ga Yuli ne aka kai hari a wata kasuwa rufaffiya da babur inda fararen hula da suka hada da mata da yara kanana suka mutu.


News Source:   ()