An kasa shawo kan gobarar daji da ke ci gaba da ci a Ostireliya

An kasa shawo kan gobarar daji da ke ci gaba da ci a Ostireliya

A jihar West Australia da ke kasar Ostireliya, an kasa shawo kan gobarar daji da ta kama tun kwanaki 4 da suka gabata inda ya zuwa yanzu ta lamushe gidaje 81 a yankin Perth.

Jami'in Hukumar Kashe Gobara ta jihar West Australia Peter Sutton ya shaida cewa, ma'aikatan kwana-kwana 500 ne suke gudanar da aiyukan kashe wutar, kuma idan aka kalli yadda ake fama da munin yanayi to gobarar za ta iya ci gaba da ci har nan da mako guda.

Sutton ya kara da cewa, gobarar ta lakume waje mai girman hekta dubu 10,kuma gidajen da suka kone sun kai 81.

Firaministan jihar WA Mark McGowan ya kira taron manema labarai a Perth inda ya sanar da cewa, tsawon kwanaki 4 kenan gobarar dajin ke balbala a kewayen birnin tare da yin barazana ga rayuwar jama'a.

Sakamakmon gobarar da ake sa ran za ta ci gaba ci har nan karshen mako saboda munin yanayi, ba a baiwa gidaje dubu 1300 hasken lantarki.


News Source:   ()