Jaridar Muslim News Nigeria ta kasar Najeriya ta baiwa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan "Lambar Girman Babban Jami'in Musulmi na Kasa da Kasa" na shekarar 2020.
Editan jaridar Muslim News Nigeria Rashid Abubakar ya bayyana wadanda aka baiwa kyaututtukan da lambobin girmamawa na #MNAwards2020.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ne aka baiwa lambar girma mafi girma mai taken "Global Muslim Personality Award" na shekarar 2020; girmamawar da ya kasance shi ke samunta shekaru uku jere ga juna tun daga shekarar 2018.
Abubakar ya bayyana cewa duk da halin Korona birus da duniya ta samu kanta a ciki, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kasance wanda ya kasance tare da gaskiya kuma ya samu nasarori akan hakan.
Ya kara da cewa matakan da Erdogan ya dauka basu kasance masu alfano a Turkiyya kawai ba, har ma ga dukkanin al'umman Musulmi baki daya.
Rashid Abubakar ya kara da cewa daga cikin nasarorin da Erdogan ya samu a cikin shekarar 2020 sun hada da mayar da Hagia Sophia Masallaci, taimakawa akan kubutar da Nagorno-Karabakh, taimakawa al'umma a cikin yanayin Korona, taimakawa al'umman Musulmi da kuma taimakawa Falasdinawa da kalubalantar ra'ayin kyamar Islama.
Haka kuma jaridar ta Muslim News Nigeria ta baiwa Ferfesa Ugur Sahin da matarsa Drk. Ozlem Tureci "Lambar Girman Jami'in Lafiya Musulmi ta Kasa da Kasa" akan sarrafa allurar riga-kafin Korona da sukayi. Haka kuma ta baiwa dan kwallon kafa Mesut Ozil lambar girman "Mashahurin Musulmin Duniya"