Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev ya kara mukamin kwamandan runduna ta musamman ta Azerbaijan daga Manjo Janar Hikmet Mirzeyev zuwa Laftanar-janar.
A cikin bayanin da Fadar Shugaban kasar Azerbaijan ta yi, an bayyana cewa Shugaba Aliyev ya yanke shawarar bai wa Mirzeyev mukamin na Laftanar janar ne kamar yadda sakin layi na 24 na Mataki na 109 na Kundin Tsarin Mulki ya tanada.