Isra’ila ta bayyana cewa a cikin awanni 24 da suka gabata an samu mutum dubu 1, 786 dauke da kwayar cutar Corona a kasar.
Dangane ga bayana da suka fito daga ma’aikatar harkokin lafiyar kasar kawo yanzu an samu mutum dubu 70,582 dauke da cutar a kasar inda kuma 509 suka mutu tun bayan bulluwar cutar a kasar a 21 ga watan Febrairu.
Mutane dubu 43,813 aka sallama daga asibiti. A yayinda al’umman kasar ke fusata akan irin matakin da gwamnatin take dauka akan yaki da corona.