An kammala aiyuka game da jirgin saman Indonesiya da ya fado

An sanar da kawo karshen aiyukan neman jikkuna da buraguzan jirgin saman fasinja da ya fado a ranar 9 ga janairu a Indonesiya.

Ministan Sufuri na Indonesiya Budi Karya Sumdi ya shaida cewa, an kawo karshen aiyukan da ake yi a yankin da jirgin ya fado.

Sanarwar da Shugaban Hukumar Bincike da Ceto Bagus Puruhito ya fitar ta ce, an saka bangarorin jikkunan mutane a ledoji 324, kuma an gano na mutane 43 daga cikin wadanda suka mutu.

Ya kuma ce, jami'ai za su ci gaba da aiki idan aka bayyana gano wani bangare na mutum ko na jirgin saman a gabar tekun.

A gefe guda, an gudanar da addu'o'i tare da ajje furenni a gabar tekun domin tunawa da wadanda suka mutu a hatsarin jirgin saman.


News Source:   ()