An kame wasu masu fafatukar kare muhalli a London

An kame masu fafatukar kare muhalli 90 karkashin inuwar Extinction Rebellion a yayin da suke gudanar da zanga zanga a London babban birnin ķasar lngila. 

Kungiyar ta Extinction Rebellion ta fara zanga zangar ne a filin shakatawar Trafalgar inda suka ci gaba har zuwa ginar Majalisar kasar .

Sun kwashi artabu da 'yan sanda ne bayan sun rufe tituna, lamarin da ya haifar da kame da yawa daga cikinsu.

A yayinda hukumar yan sanda suka bayyana kame mutum 90 daga cikin masu zanga zangar, kungìyar ta Extinction Rebellion ta bayyana cewa zata co gaba da zanga zangar har tsawon kwanaki goma.

 


News Source:   ()