An sanar da mutuwar mutum daya sakamakon harin da aka kai masa da wuka a birnin Vancouver dake kasar Kanada.
An sanar da kai masa harin ne a gaban dakin karatun dake kusa da wata kasuwa a birnin Vancouver.
A harin baya ga rasuwar mutum daya wasu shida kuma sun jikkata.
An dai yi nasarar kame wadanda ake zargi da kai harin tuni kuma an fara bincike akan lamarin.
Firaiministan kasar Justin Trudeau ya mika sakon jaje tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka raunanan.