Jami'an tsaro masu gadin gabar tekun Libiya sun kama bakin haure kimanin 500 wadanda ke kan hanyarsu ta tsallaka Bahar Rum zuwa Turai ba bisa ka'ida ba.
Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta bayyana cewa an kame bakin haure 310 a shekaran jiya inda kuma aka kame wasu bakin hauren 173 aka kuma mayar dasu kasar Libiya.
Daga cikin bakin hauren akwai mata da yara an bayyana cewa suna cikin mawuyacin hali.
A 'yan shekarun nan Libiya ta kasance gabar da bakin hauren da suka tserewa rikici da talaucin kasashensu daga Afirka ke bi domin shiga Nahiyar Turai.