An kame bakin haure 16 yayinda suke yunkurin shiga Turkiyya ta barauniyar hanya

An kame bakin haure 16 yayinda suke yunkurin shiga Turkiyya ta barauniyar hanya

An sanar da kame wasu bakin haure 16 da suka yi yunkurin kutsawa Turkiyya ta barauniyar hanya daga Siriya.

Ma'aikatar tsaron kasar Turkiyya ce ta sanar da cewa,

“A yankin Reyhanli dake karkashin gundumar Hatay, jami'an tsaro sun kame wasu bakin haure 16 a yayinda suke neman shigowa kasarmu ta barauniyar hanya. Binciken da aka yi ya tabbatar da cewa biyu daga cikinsu mambobin Heyet Tahrir Damascus ne, biyu kuma mambobin kungiyar ta'addar DEASH"

 


News Source:   ()