Jami'an tsaro a Amurka sun kama wani mutum a kusa da gidan Mataimakiyar Shugaban Kasar Kamala Harris.
Ma'aikatan tsaro na farin kaya ne suka kama mutumin da 'yan sanda su ke nema a kusan da gidan Harris.
'Yan sanda sun kuma gudanar da bincike a cikin motar mutumin da ya tsaya a wani waje da ke kusa da gidan.
An samu bindiga da harsashai a motar mutumin.
Mutumin da aka kama na da shekaru 31 kuma ya shiga hannu bayan bayanan sirrin da 'yan sandan Texas suka bayar.
Mataimakiyar Shugaban Kasar Amurka da mijinta ba sa gidan saboda 'yan gyare-gyare da ake yi.