A cewar alkaluman da hukumar ta ke wallafawa a shafinta na X, a ranar Alhamis din da ta gabata mutane 538 suka kama, sai suka sake kama wasu 593 a ranar Juma’a, sannan mutane 286 a ranar Asabar.
Har wa yau, jami’an hukumar shigi da fici sun kama bakin haure 956 a ranar lahadi, sai kuma kame mafi girma da suka yi a jiya litinin na mutane dubu daya da 179.
Gwamnatin Trump dai ta sha alwashin kwashe bakin haure da kuma masu neman mafaka ba bisa ka’ida ba a ƙasar, tun bayan rantsar da shi ya ake kama sama da adadin waɗanda aka saba kamawa a kowace rana a gwamnatin magabacinsa Biden, wanda bai wuce mutane dari 310 ba.
Wasu daga cikin bakin haren Guatemala da aka maidasu gida daga Amurka. © Скриншорт з відео ReutersTuni dai Amurka ta fara turawa da su wasu ƙasashe, domin ko a jiya litinin sai da wani jirgin soji ya kai wasu ƙasar Guatemala, kwana guda bayan musayar yawu da Colombia, da ta ki amince wa wani jirgi ɗauke da ƴan ciranin da Amurka ta kwaso ya sauka a cikinta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI