An kama Ministan Muhalli na Tunisiya wanda aka kora daga aiki

Ministan Muhalli da Harkokin Cikin Gida na Tunisiya, Arvi wanda aka kora daga aiki a farkon makon nan, da wasu mutane 7 gami da manyan jami'an ma'aikatar, an kame su a wani bangare na binciken abubuwa masu guba da aka gano a kan wani jirgin dakon kaya na Italiya da ya zo ƙasar.

Kakakin Kotun Farko ta Susa, Jabir al-Gunaymi wanda ya binciki bayanan ya bayyana cewar an kame mutane 8, ciki har da tsohon Ministan Muhalli da Harkokin Cikin Gida, Mustafa al-Arvi.

Gunaymi ya bayyana cewar akwai mutane 23 da ake tuhuma a cikin karar, wadanda suka hada da manyan ma’aikatan ma’aikatar, an bayar da shaidar mutane 10 amma ba a kamasu ba, an saki 4 daga cikinsu kuma daya daga cikin wadanda ake tuhuma ya gudu.

Firaministan Tunisiya, Hisham al-Mesishi a yammacin ranar Lahadin da ta gabata ya sanar da cewa an kori Mustafa al-Arvi, Ministan Muhalli da Harkokin Cikin Gida ba tare da bayar da wani dalili ba.

Kotun da ke binciken kara a Susa ta ba da umarnin tsare Arvi a jiya.

Gunaymi ya bayyana cewar tun da farko an kira Arvi ne a matsayin mai bayar da shaida a cikin binciken amma bai zo ya bayar da shaida ba, kuma yayin da aka ci gaba da bincike, akwai shaidar cewa yana da alaka da abun da ya faru.

A watan Yulin da ya gabata, a garin Susa da ke gabar ruwa a kasar Tunisiya, hukumomin tashar jirgin ruwa sun gano abubuwa masu guba da ya sabawa ka’idojin kasa da kasa a cikin kwantena da ke kan wani jirgin ruwa da ke dauke da shara da ta taso daga kasar Italiya inda suka tsare jirgin. 

Lamarin ya gamu da martani daga jama'a bayan da manema labarai suka watsa labarin.


News Source:   ()