Shugaban kungiyar na duniya, Christos Christou, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, yana mai cewa akwai dokokin kare hakkin dan adam da kuma dokokin jin kai da aka take a Gaza.
Ya ce kungiyar ta MSF ta rasa ma’aikatanta har guda takwas a Gaza, sannan an kasha sama da jami’an agaji sama da 1,000.
MSF ta ce nan gaba kadan za a shafe dukkanin ayyukan da suka danganci harkokin kiwon lafiya a Gaza.
“Ana bukatar kai daukin gagaggawa kama daga bangaren lafiya da kuma abinci a Gaza”, in ji Christos Christou.
Ya ce babu damar kai kayayyakin agajin jin kai, saboda an hana jami’ai shiga, kuma har yanzu ba a fada musu dalilin yin hakan ba.
Christos Christou, ya kara da cewa yanzkin na Gaza na bukatar sabbin asibitoci domin kula da wadanda ke cikin mummunan yanayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI