An kaiwa wasu Masallatan Juma'a hari a Afganistan

Mutane 11 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kai wa wasu Masallatan Juma'a 2 da ke jihohin Pervan da Host na Afganistan.

Kakakin Fadar Gwamnan Pervan Wahide Shekar ya fadi cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai wa Masallacin Juma'a da ke kauyen Hilazey hari.

Shehkar ya ce maharan sun kashe fararen hula 8 tare da jikkata wasu 5.

Kakakin Fadar Gwamnan Host Talip Mengel ya ce an kai hari kan Masallacin Juma'a na kauyen Kurchak da ke gundumar Sabari inda aka kashe fararen hula 3 tare da jikkata wani farar hula 1.

Babu wanda ya dauki alhakin kai hare-haren 2.


News Source:   www.trt.net.tr