An sanar da cewa harin bam da aka kai wa matocin sojoji a Mogadishu babban birnin Somaliya ya yi sanadiyar rayukan mutane uku da suka hada da sojoji biyu.
Harin lamari ne da aka kai da zummar hallaka manyan sojojin kasar.
A harin dai ba'a yi nasarar samun manyan sojojin ba sai dai mutum 3 da suka hada da sojoji biyu sun rasa rayukansu.
Kawo yanzu dai ba a dora alhakin kai harin akan kowa ba.