Masallacin Ibni Sina, a yankin Breton da ke arewa maso yammacin Faransa, ya fuskanci mummunar kyamar Musulunci da wariyar launin fata a karo na biyu cikin kwanaki 20.
Bayanan da aka rubuta a bangon Masallacin garin Rennes an bayyana cewa "Ku farga Faransawa", "Muna yi muku gargaɗi, kwararar 'yan gudun hijira kisa ne","Ba maganar yada addinin Musulunci."
Majalisar musulinci ta Faransa tare da kwamitin hadin kan kungiyoyin musulmin Turkiyya na Faransa sun yi Allah wadai da harin nuna wariyar launin fata da kyamar addinin Islama da aka kaiwa masallacin.
Masallacin na Ibni Sina shi ma an kuma kai masa hari makamancin wannan a ranar 11 ga Afrilu, kuma Ministan Cikin Gida Gerard Darmanin ya ziyarci masallacin, yana mai cewa ba za a amince da irin wanan tabi'ar ba.
An kuma kona Masallacin Arrahma da ke Nantes dake Faransa a daren 9 ga watan Afrilu