An sanar da cewa wasu masu kyamar Islama sun kaiwa wani Masallaci mallakar kungiyar Haddin kan Turkawa Musulmi (DITIB) hari da duwatsu a garin Cologne dake Jamus.
Kasar da aka kwashe makonni 8 guraren ibadu na rufe domin yakar kwayar cutar corona ne aka farfasa gilasai da kofofin wani masallaci a ranar da gwamnatin kasar ta bayar da izinin bude guraren ibadu.
Kamarar tsaron masallacin ta dauke yadda mutanen suka rinka jifar masallacin da duwatsu da misalin karfe 01.13 na dare.
An bayyana cewar an ga mutane biyu yayinda da suke ta jefawa masallacin duwatsu.
Shugaban masallacin hukumar DİTİB dake Chorweiler İbrahim Altun, ya tabbatar da cewa an sanar da hukumar 'yan sanda lamarin kuma tuni sun fara bincike.
Altun, ya bayyana fatan kama wadanda suka aikata aika-iakan da kuma gamuwa da fushin hukuma nan bada jimawa ba.