An kaiwa ma'aikatun Amurka harin yanar gizo daga Rasha

An kaiwa ma'aikatun Amurka harin yanar gizo daga Rasha

Ma'aikatar Shari'ar Amurka ta sanar cewa harin satar bayanai ta yanar gizo mai taken SoberWinds da aka kaiwa ma'aikatun kasar Amurka a shekarar bara hackers na intanet din kasar Rasha ne suka aitkashi.
A cikin sanarwar da ma'aikatar ta fitar, an bayyana cewa an kai hare-haren na SolarWinds ta yanar gizo tsakanin 7 ga watan Mayu zuwa 27 ga watan Disamba na shekarar 2020.
A hare-haren da aka kaiwa ma'aikatun masu gabatar da kara a fadin kasar kaso 80 cikin darinsa email din ma'aikatan ne aka kaiwa harin da kuma na akallan masu gabatar da kara 27.

An bayyana cewa an kai harin ne akan  imel din ofishin masu gabatar da kara domin za'a  iya samun bayanai tare da babban sirri.

Kamfanin fasahar Amurka na Microsoft ya sanar a ranar 28 ga Mayu cewa masu fashin kwamfuta na SolarWinds da ke Rasha sun kai hari kan ma'aikatu 150.

A cikin sanarwar da kamfanin Microsoft ya fitar, an lura cewa masu kutse ta yanar gizo sun kai hari kan cibiyoyin gwamnati da kuma cibiyoyin bincike da kungiyoyi masu zaman kansu.


News Source:   ()