An sanar da kai harin ta'addanci ga ma'aikatan wani kanfanin Turkawa dake Somaliya lamarin da ya yi sanadiyar rayukan mutum hudu da suka hada da Baturke guda da kuma raunanan wasu Turkawa hudu.
Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya ta sanar ta bayyana cewa za ta cigaba da kula da lafiyar Turkawa hudun da suka raunana.
Sanarwar da ta kalubalanci harin tare da yin Allah wadai dashi ta kara da cewa,
"Muna masu matukar yin Allah wadai da harin ta'addancin da aka kaiwa ma'aikatan kanfanin titi mallakar Turkawa a yayinda suke aiki akan titin Mogadishu-Afgoye dake Somaliya. Muna fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka raunana da kuma fatan samun rahamar Allah ga wadanda suka rigamu gidan gaskiya, muna kara tabbatar da cewa Turkiyya zata cigaba da kasancewa da Somaliya a koda yaushe"