An sanar da cewa 'yan fashin teku sun sake kaiwa wani jirgin ruwan Kargo hari a yankin Gulf din Guinea dake Yammacin Afirka.
Kamar yadda mujallar dake yada bayanai game da harkokin teku ta "Maritime Bulletin" ta yada a shafinta na yanar gizo, a yankin mashigar Togo an kaiwa wani jirgin ruwan kargo mai dauke da tutar Amurka hari.
An bayyana cewa an kaiwa jirgin hari ne yayinda yake tashi daga tsibirin Canary zuwa Lagos dake kudancin Najeriya tare da sauya masa hanya.
Kawo yanzu dai ba a samu bayani game da lafiyar ma'aikata jirgin ba.