An kashe 'yan ta'addar Daesh 3 sakamakon farmakin da jami'an soji suka kai musu a jihar Salahaddin da ke Iraki.
Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Tsaro ta fitar ta bayyana cewa, dakarun sojin kasar sun fara kaiwa 'yan ta'addar Daesh farmakai a arewacin jihar.
Sanarwar ta kara da cewa, an kashe 'yan ta'addar Daesh 3 tare da jikkata sojojin Iraki 2 sakamakon arangamar da aka yi.
An bayyana cewa, an bayar da gudunmowa da jiragen yaki na sama a yayin kai farmakan.
A watan Yunin 2014 'yan ta'addar Daesh suka kwace iko da jihohin Mosul, Salahaddin da Anbar da ke Iraki, haka zalika sun sake kwace iko da wasu bangarori na jihohin Diyala da Kerkuk.
Tsohon Firaministan Iraki Haydar Al-Abadi a ranar 9 ga Disamban 2017 ya sanar da kawo karshen kungiyar Daesh a kasar.
Duk a an dauki tsawon shekaru 3 da magance kungiyar, amma daga loakci zuwa lokaci tana kai hari a Iraki.