An kai samame gidajen dan adawa Aleksey Navalniy

An kai samame gidajen dan adawa Aleksey Navalniy

A Rasha 'yan sanda sun kai samame gidajen dan adawa Aleksey Navalniy da aka tsare da kuma ofishin Gidauniyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa wanda ya kafa.

Daraktan Gidauniyar ta Yaki da Cin Hanci da Rashawa, Ivan Jdanov wanda aka sanya a cikin jerin sunayen "wakilai na kasashen waje" daga Ma'aikatar Shari'a ta Rasha, ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Twitter inda ya bayyana cewar an bincika gidajen Navalniy, wanda aka tsare d​​a na matarsa da ke Moscow, babban birnin Rasha da Gidauniyarsa ta Yaki da Cin Hanci da Rashawa.

Da Jdanov ya ke bayyana cewar 'yan sanda sun shiga gidajen ta hanyar fasa kofofi, ya ce an karya dokoki da matakan yaki da annoba a binciken da aka gudanar.

A ranar 23 ga watan Janairu, dubun-dubatar mutane sun halarci zanga-zangar da aka gudanar ba da izini ba don sakin Alexei Navalniy, inda aka tsare fiye da mutane dubu 3.

Kakakin Kremlin (Fadar Shugaban kasar Rasha), Dmitriy Peskov ya bayar da hujjar cewa zanga-zangar nuna goyon baya ga Navalniy haramtacciya ce kuma ba za a amince da ita ba.

Masu zanga-zangar na Navalniy sun sanar da cewa za su sake gudanar da zanga-zanga a ranar 31 ga Janairu.


News Source:   ()