A harin ta'addancin da aka kai da mota dauke da bama-bamai a yankin Afrin dake Arewacin Siriya an bayyana cewa mutum 6 sun rasa rayukansu inda wasu 25 suka jikkata.
An ajiye motar ne dankare da bama-bamai a yankin mai kanfuna a Afrin dake arewacin Siriya.
A bayanan da aka fara fitarwa harin ta'addanci ya yi sanadiyar rayukan farar hula 6 da kuma raunana wasu 25 wadanda 10 daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Ana dai fargaban cewa yawan wadanda zasu iya rasa rayukansu ka iya karuwa.
Jami'an kashe gobara sun kai dauki a yankin da bam din ya tashi wanda aka ji kararsa a dukkanin garin Afrin.
An sanar da cewa abin fashewar ya kai nauyin kilo 50.
Jami'an tsaron dake gudanar da bincike a yankin da lamarin ya afku suna hasashen cewa kungiyar ta'addar YPG/PKK ce ta kai harin.
A yankin Afrin dai a ranar 18 ga watan Maris din shekarar 2018 ne aka kaddamar da farmakin reshen zaitin inda aka kubutar da yankin daga hannun kungiyar ta'addar YPG/PKK.