An kai mummunan harin ta'addanci a Afghanistan

An kai mummunan harin ta'addanci a Afghanistan

An sanar da rasa rayukan mutum 8 da raunanan 53 a wani harin da aka kai da mota dauke da bama-bamai a ofishin 'yan sanda dake jihar Herat a kasar Afghanistan.

Walin Herat, Sayed Wahid Katail ya sanar da cewa an kai harin ne da zumma far ma ofishin 'yan sandan dake yankin.

A harin hadi da farar hula mutum 8 sun rasa rayukansu 53 sun raunana daga cikinsu 6 na cikin mawuyacin hali.

An ji karar harin a kusan dukkanin yankunan dake yankin. Lamarin da ya haifar da lalacewar gidaje da dama.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin amma mai magan da yawun rundunar tsaron Tarik Aryen ya daura alhakin kai harin akan Taliban.

A dayan barayin kuma ana ci gabba da zaman sulhu tsakanin gwamnati da kungiyar Taliban a Doha babban birnin kasar Katar.

 


News Source:   ()