An kai mummunan hari a Afghanistan

An kai mummunan hari a Afghanistan

An sanar da cewa a harin da aka kai da mota dauke da bama-bamai a garin Gazne dake kasar Afghanistan mutum 23 sun rasa rayukansu inda wasu 16 suka jikkata.

Dangane ga bayanan da suka fita daga kafar yada labaran "Tolo News" mai magana da yawun Walin Gazne Wahidullah Jumazada ya sanar da cewa wata mota dauke da bama-bamai ta kai hari a wata ma'aikata dake garin.

Jumazada ya kara da cewa a harin mutum 23 sun rasa rayukansu inda kuma wasu 16 suka raunana.

Kawo yanzu dai ba'a dora alhakin harin da aka kai a inda kwamandoji suke akan kowa ba.

 


News Source:   ()