An kai karar Girka ga kotun ICC akan muzgunawa ‘yan gudun hijira

An kai karar Girka ga kotun ICC akan muzgunawa ‘yan gudun hijira

Wata kungiya mai zaman kanta ta gabatar da kara ga kotun Binciken Miyagun Laifuka ta Kasa da Kasa wato ICC domin a gudanar da bincike akan muzgunawa ‘yan gudun hijira da Girka ke yi.

A ‘yan watannin da suka gabata an yi ta rawaito cewa Girka na kora ‘yan gudun hijira zuwa cikin tekun Ajiyan.

Cibiyar Adalci da Doka ta Siriya ta yi korafin yadda ake muzgunawa ‘yan gudun hijira a kasar Girka. Ta bayar da misalai yadda jami’an tsaron Girka ke amfani da barkonon tsohowa akan ‘yan gudun hijiran da kuma irin yadda aka bar sansanonin ‘yan gudun hijrar dake kasar cikin halin ko in kula.

Mohammad Al-Abdallah, shugaban kungiyar ya bayyana cewa wannan ne dai mataki na farko da suka dauka akan irin wulakantar da ‘yan gudun hijira da ake yi a Turai.


News Source:   ()