An kai harin ta'addanci a Afrin din Siriya

An kai harin ta'addanci a Afrin din Siriya

An sanar da cewa tashin wasu bama-bamai a cikin wata mota da aka yi parkin a gefen hanya a garin Afrin dake arewacin Siriya ya yi sanadiyar raunakan mutane hudu da suka hada da yara.

Baya ga tarwatsewar motar tashin bam din kuma ya barnata kaddarorin dake kusa da ita.

Ana zaton cewa kungiyar ta'addar YPG/PKK ce ta kai harin.

Kungiyar ta'addar YPG/PKK dake mamayar yankin Tel Rıfat da Münbiç ta kasance tana yawan kai hare-hare a yankunan Bab, Azez, Cerablus da Afrin.

 


News Source:   www.trt.net.tr