An sanar da cewa harin da aka kai da mota dauke da bama bamai a wani barikin sojoji dake jihar Gazne a kasar Afghanistan ya yi sanadiyar rayukan sojoji uku.
Mai magana da yawun Walin Gazne Wahidullah Jumazadah ya bayyana cewa an kai hari da mota dauke da bama-bamai a barikin sojan dake Molla Nuh Baba.
Cumazadah, ya bayyana cewa a harin sojoji uku sun rasa rayukansu wasu biyu kuma sun raunana.
Kawo yanzu dai ba a dora alhakin harin akan kowa ba.