Harin ta'addancin da aka kai a garin Bab dake kasar Siriya da mota dauke da bama-bamai ya yi sanadiyar rauwar farar hula daya da kuma raunanan wasu hudu.
An ajiye mota dankare da bama-bamai a yanki mai kanfuna da rundunar sojan Turkiyya suka kauda 'yan ta'adda a Farmakin Garkuwar Firat da suka gudanar daga watan Agustan 2016 zuwa Maris 2017.
A harin da 'yan ta'addan suka kai an bayyana rasa rayuwar mutum daya da kuma raunanan wasu hudu.
Jami'an kashe gobara sun dauki matakan kashe watar da ta kama bayan tashin bam din.
Gobarar ta yi sanadiyar hasarar dukiya ga shaguna mafi kusa da dama.
Jami'an tsaron dake gudanar da bincike a inda lamarin ya afku sun bayyana cewa ga dukkan alamu kungiyar ta'addar YPG/PKK ce ta kai harin.