An kai harin kunar bakin wake a Somaliya

An kai harin kunar bakin wake a Somaliya

A cewar rahotannin farko mutane 8 ne suka mutu a wani harin kunar bakin wake da aka kaiwa jerin gwanon motocin gwamnati a Mogadishu, babban birnin Somaliya.

A wata mahada da ke da cunkoson jama'a a cikin birnin, yayin da ayarin gwanon motocin gwamnati ke wucewa, wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da bam daga cikin motan da yake.

Wani shaidar gani da ido da ke sanar da kamfanin dillacin labaran Birtaniya na Reuters ya bayyana cewa, mutane 8 ciki har da mace sun rasa rayukansu a harin.

Yayin da kamfanin dillacin labarai na kasar ya sanar da cewa Ferhan Qaole, babban jami’in ‘yan sanda a cikin ayarin, ya tsere ba tare da jin rauni ba, har yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin.

Kungiyar ta'adda a kasar, al-Shabab, ta kan shirya kai hare-hare a yankuna da dama, musamman a Mogadishu babban birnin kasar.


News Source:   ()