Mutane 15 sun samu raunuka sakamakon harin bam da aka kai Kabul Babban Birnin Afganistan kan wata mota da ke dauke da jami'an Ma'aikatar Sadarwa ta kasar.
Kakakin helkwatar 'yan sandan Kabul Firdaus Faramarz ya shaida cewa, an kai harin bam kan mota dauke da jami'an Ma'aikatar Sadarwa ta kasar.
Faramarz ya ce, an jikkata mutane 15 sakamakon harin bam din.
A 'yan kwanakin nan ana yawan kai hare-hare kan 'yan jaridu, masu fafutuka, Malaman Addini, ma'aikatan gwamnati da jami'an tsaro a Afganistan.
Gwamnatin Afganistan na zargin Taliban da kai hare-haren, amma Taliban na cewa ba ta da alaka da su.