Fararen hula 5 sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da aka kai a jihar Kandahar da ke kudancin Afganistan.
Kakakin 'yan sandan Kandahar Janal Nasir Barikzey ya shaida cewa, wani bam da aka binne a yankin Gec Kariz na gundumar Meyvend ne ya fashe a lokacin da mota dauke da fararen hula take wucewa.
Brikzey ya shaida cewa, fararen hula 5 sun mutu, wasu 18 kuma sun jikkata.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.