A Girka, an kai hari kan sansanin 'yan gudun hijira da yara kanana da babu masu kula da su su ke zaune.
Labaran da jaridun Girka suka fitar sun bayyana cewa, a daren Lahadin da ta gabata ne wasu masu nuna wariyar launin fata da kyamar baki suka taru a gaban sansanin da ke karkashin kulawar Cocin yankin Oreokastro dauke da wukake, sanduna da adduna.
Mutanen sun dinga fadin maganganun nuna wariya da kyamar baki, sun kuma yi kokarin shiga bangaren da yaran su ke zaune amma jami'an tsaro da ma'aikatan wajen suka hana su.
Lauyan sansanin Thodoris Karayannis ya fadi cewa, za su shigar da kara nan da wani dan lokaci.
A shekarun 2016 da 2017 an kai hari kan 'yan gudun hijira da ke zama a sansanin wanda hakan ya janyo babban rikici.