An kai hari kusa da sansanin MDD a Somaliya

An bayyana cewa mutun uku sun rasa rayukansu a harin da roka da aka kai ta ga ginukan Majalisar Dinkin Duniya da Tarayya Afirka dake Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.

Jami'in yan sanda a yankin Dharkinley wato Andi Yusuf ya bayyana cewa an kai hari a sansanin Halane na Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka.

Yusuf ya kara da cewa a harin da aka kai da rokoki ta sama kasancewar samun wasu gidaje dake kusa da sansanin ya yi sanadiyar rayuwar mutane uku da raunana wasu biyar.

An dai dora alhakin harin akan kungiyar ta'addar Ashabab. 

 


News Source:   ()