An kai hari kan wani Masallaci a Jamus

An kai hari kan wani Masallaci a Jamus

Magoya bayan kungiyar 'yan ta'addar aware ta PKK/YPG sun rubuta sunan kungiyar a bangon wani Masallaci da ke garin Dresden na kasar Jamus.

Taron jama’ar da ke zuwa sallar asuba ne suka lura da rubutun batanci ga Musulunci da wani ko wasu mutane da ba a san ko su waye ba suka yi daddare a bangon Masallacin Fatih, wanda ke da alaƙa da Hukumar Hadin Kan Islama ta Ma'aikatar Addinin Turkiyya (DITIB).

Da farko dai, an sanar da mahukuntan Masallacin, sannan aka sanar da 'yan sanda game da abin da ya faru.

'Yan sanda, wadanda suka binciki Masallacin da ke kan titin Huhndorfer inda mutane 300 ke iya yin salla a lokaci guda, sun fara bincike ta hanyar daukar rahotuna.

A shekarar 2016 ma an kai hari da bama-bamai kan Masallacin, kuma an yanke wa Nino K., wanda aka gano a matsayin maharin, hukuncin shekara 9 da watanni 8 a kurkuku.

A harin da aka kai kan Masallacin a bara kuma, an farfasa tagogi kuma an lalata kayan da ke cikin Masallacin.


News Source:   ()