Mutane 4 ne suka rasa rayukansu a wani hari da adda da wani da ba a san ko waye ba ya kai wata makarantar renon yara da ke jihar Santa Catarina na Brazil.
Jami’an jihar Santa Catarina sun bayyana cewa wani da ba a san ko waye ba ya kai hari a wata makarantar renon yara da ke jihar da adda.
Ministan Ilimi na jihar Santa Catarina, Gisela Herman ya bayyana cewa mutane 4 da suka hada da yara 3 da malami sun mutu a harin.
A cikin labaran da kafofin yada labarai na cikin gida suka rawaito, an bayyana cewa daga cikin yara a makarantar akwai jariri ɗan watanni 6 da yara har zuwa shekara 3.