'Yan fashin teku sun kai hari kan jirgin ruwan Hukumar Kasuwanci ta Ingila (UKMTO) a gabar tekun kudancin Yaman.
Sanarwar da aka fitar a shafin yanar gizon UKMOT ta ce an kai hari kan jirgin a gabar tekun garin Aden na Yaman.
Ba a bayar da cikakken bayanin su waye suka kai harin ba, kuma babu wanda ya dauki nauyin kai shi.
Labaran da jaridun Yaman suka fitar na cewa jirgin da aka kai wa harin mallakar kamfanin Stolt na Ingila ne kuma 'yan fashin teku ne suka kai masa harin.